Takarar neman maye gurbin firaministan Japan
September 8, 2025Tsohon ministan harkokin wajen kasar Japan, Toshimitsu Motegi ya zama mutum na farko da ya nemi 'yan majalisar dokoki na jam'iyya mai mulki ta Liberal Democratic Party (LDP) su ba shi damar zama sabon Firaminista, domin ya maye gurbi Firamnista Shigeru Ishiba mai barin gado wanda ya bayyana yin murabus daga kan mukamun.
Karin Bayani:Firaministan Japan Shigeru Ishiba ya yanke shawarar yin murabus
A wannan Lahadi da ta gabata Firaminista Shigeru Ishiba ya bayyana murabus daga kan madafun ikon kasar wadda take matsayi na hudu wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen duniya.
Ita dai jam'iyyar LDP ta yi jagoranci a mafi yawan lokaci tun bayan yakin duniya na biyu, kuma Motegi mai shekaru 69 da haihuwa yana ya ce yana fata kan iya jagoranci jam'iyyar da magance matsalolin da ake fuskanta, sai dai ana sa ran samun karin mutane da za su nemi shugaban jam'iyya mai mulkin kasar ta Japan, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar.