SiyasaAfirka
An fara makoki a Ghana kan mutuwar ministoci a hadarin jirgi
August 7, 2025Talla
Shugaban Ghana John Dramani Mahama, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku, sakamakon mutuwar ministocin kasar biyu, da wasu mukarraban gwamnati, sanadiyyar hadarin jirgi mai saukar ungulu na rundunar sojin kasar, wanda ya tashi daga Accra babban birnin kasar zuwa yankin Obuasi na lardin Ashanti.
Karin bayani:Ministocin Ghana biyu sun mutu a hadarin jirgin sama
Daga cikin mutane 8 din da suka rasa rayukansu a hadarin na ranar Laraba, akwai ministan tsaro Edward Omane Boamah da takwaransa na muhalli Ibrahim Murtala Muhammed, sai mataimakin shugaban jam'iyyar NDC mai mulkin kasar Samuel Sarpong.
Sauran sun hada mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro Muniru Mohammed da kuma ma'aikatan jirgin hudu.