SiyasaAfirka
An daure jami'in lafiya kan tunzura gwamnati a Côte d'Ivoire
July 22, 2025Talla
Hukuncin kotun na zuwa watanni gabanin gudanar da babban zaben shugaban kasar da za a gudanar a karshen watan Oktobar 2025, wanda kuma 'yan adawa ke sukar manufofin gwamnatin kasar kan murkushe masu hamayya da Mr. Ouattara.
Karin bayani:Jam'iyyar na son Shugaba Ouattara ya zarce kan mulki
Ma'aikacin lafiyar Tokpa Flan Japhet mai shekaru 43 zai shafe shekaru uku a gidan yari ko kuma ya biya tarar dala $8,500, duk da cewa lauyansa ya nemi afuwa kan furucin da ma'aikacin lafiyar ya yi a shafinsa Facebook.
Karin bayani: Tsohon shugaban Côte d'Ivoire ya amince da tsayawa takara
Har yanzu dai Alassane Ouattara mai shekaru 83 bai furta cewa ko zai tsaya takara ba, duk da cewa yana fuskantar matsin lamba daga 'ya'yan jam'iyyarsa kan bukatar hakan.