Kwango da Ruwanda sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya
June 28, 2025Talla
An cimma wannan matsayar ce mai matukar muhimmanci karkashin jagorancin Washington, kamar yadda sakataren harkokin wajen Amirka Marco Rubio ya tabbatar.
Da yake tsokaci a kan wannan yarjejeniya Shugaba Donald Trump ya ce kissan al'umma da ma lalata dukiyoyinsu ya kawo karshe, kuma daukacin yankin ya shiga wani sabon babi na ci gaba da zai bude kokfofin damamaki da dama.
A watan da ya gabata Trump ya bayyana cewar muddin aka cimma yarjejemniya zaman lafiya, hakan zai bai wa kamfanonin kasarsa da ma na kasashen Turai damar zuba miliyoyin daloli a harkar ma'adanan kasar.
Tuni kasashen duniya suka yi maraba da wannan mataki da aka cimma da ma fatan ganin an mutunta shi.
Karin Bayani: Ina makomar wadanda M23 ta mayar Ruwanda?