An ceto kananan yaran da aka yi garkuwa da su a Kamaru
August 22, 2025Tun bayan sace yaran a kan hanyarsu cikin wata motar bas da ke tafiya daga garin Kousseri zuwa Maroua, hukumomin Kamaru ba su yi wani karin haske ba har sai a ranar Alhamis, lokacin da gwamnan yankin Arewa Mai Nisa, Midjiyawa Bakari, ya bayyana a wani bidiyo a shafukan sada zumunta cewa dakarun sojojin Kamaru tare da rundunar yaki da ta'addanci da ta hada da sojoji daga kasashen makwabta Najeriya da Chadi suka ceto yaran. Sai dai ministan y ace abin takaici daya daga cikin yaran ya mutu a yayin da yake hannun ‘yan bindigar da suka tsere da su zuwa wani yanki na Najeriya.
Karin bayani: An ceto daliban jinya 20 a Benue
Gwamnan ya kara da cewa an kama mutum 50 a cikin samamen, amma bai yi bayani kan yadda aka yi garkuwa da yaran ba. Boko Haram ta dade tana tayar da kayar baya a arewa maso gabashin Najeriya tun daga 2009, lamarin da ya bazu zuwa kasashe makwabta ciki har da arewacin Kamaru.