An cafke 'yan ci-rani 150 a arewacin Nijar
November 2, 2013A fadar hukumomin an cafke yan ci-ranin ne a ranakun Jumma'a da kuma jiya Asabar. Wata kafa ta tsaro ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, akasarin wadanda aka kama a hamadar Sahara maza ne da kuma yara kanana. Tuni ma dai aka tsare su a cibiyar jandarmomi da ke garin Arlit.
Da ma dai hukumomin Yamai sun sanar da cewa za su dau matakan ba sani ba sabo kan duk wadanda za a samu da hannu a kwasar 'yan ci-rani daga arewacin Nijar zuwa kasar Aljeriya ko kuma Libiya. Tuni ma dai suka sha alwashin rufe daukacin sansanonin 'yan ci-rani da ke arewacin kasar ta Nijar.Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne kwanaki kalilan, bayan da aka gano gawarwakin 'yan ci-rani da kishiruwa ya kashe a hamadar Sahara, a kokarinsu na zuwa Aljeriya domin inganta rayuwarsu.
A yanzu haka dai akwai 'yan ci-rani kimanin dubu biyar daga kasashe dabam-dabam na Afrika, da ke a wasu haramtattun sansanonin 'yan gudun hijira a Agadez da ke arewacin Nijar.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman