Najeriya: Sabon tsarin biza ta Intanet
April 10, 2025Sabon tsarin ba da takardar izinin shiga Najeriyar ta intanet ya kasance mai cike da sauye-sauye masu yawan gaske duka a kokari na saukaka wa masu son ziyaratar Najeriyar da kan yi koke na daukan lokaci mai tsawo saboda tilas sai sun je ofishin jakadancin Najeriya da ke kasashen da suke kafin samun takaradr biza. Duk wannan a yanzu ya sauya domin sabon tsari ne da na'ura ce ke aikin tun daga neman takardar har zuwa bada ita. Dr Tunji Ojo shi ne ministan kula da harkokin cikin gida na Najeriyar ya bayyana yadda tsarin yake a yanzu.
‘' Daukacin batun shi ne a yanzu mun mayar da aikin kula da amincewa da ba da takardar biza zuwa ga Najeriya, domin da tsarin da muke da shi babu wani kulawa ofisoshin jakadanci ne ke komai a can. A yanzu da zarar ka aika da takardar neman bisa ta intanet tsarin da muka samar ne zai karbi takardar, mun hada manhajar da hukumomin tsaro na kasa da kasa da za su duba cancantarsa.''
Bullo da wanna sabuwar hanya ta ba da biza ta intanet muhimmin mataki ne da masu neman shigowa Najeriyar suka dade suna neman kai wa ga haka, saboda matsala ta cuku-cuku, jinkiri da sukan fuskanta abin da ke kawo cikar a fanonin da dama. A bangare guda akwai batu na kara kaimi wajen sa ido a kan bakin da ke shigowa su fake suna aikata miyagun laifuffuka a kasar wanda sakaci ne da aka samu a fanin samun takardun izinin shigowa Najeriyar. Farfesa Ghali Sherif kwararre a fanin shige da ficen kasa da kasa a Najeriyar ya ce tsarin yana da kyau.
Duk da bullo da tsarin ba da biza da zarar an sauka a tashoshin jiragen saman Najeriya bai canza jinkirin da ake fsukanta ba. Najeriyar dai ta bi sahun wasu kasashen duniya ne wajen zamunatar da harkar ba da takadar izinin shiga kasar ta intanet din, tsarin da ya bai wa masu shigowa kasar karin kafofin da za su nemi izinin shigo Najeriya nan take ta intanet a ba su. Mahukuntan kasar sun bayyana cewa bayaga saukaka tsarin zai ma bunkasa tattalin arziki.
Ana cike da fatan samun sauyi mai ma'ana na zamantara da tsain samun takardar biza don shiga Najeriyar ta intanet a cikin sao'i 24 a sabon yanayi da ya dace da zamani irin na kasashen da suka ci gaba, duk da kalubalen da ake tsoron fuskanta a farkon aiki da tsarin.