SiyasaMexiko
An bude wuta kan wata 'yar TikTok a Mexico
May 15, 2025Talla
Kisan na 'yar Tiktok din ya harzuka al'ummar kasar ta Mexico. Baturen 'yan sandan yankin Zapopan ya bayyana wa manema labarai cewa sun kaddamar da bincike kan kisan da aka yi wa 'yar TikTok din kuma sarauniyar kyau Ms. Marquez.
Karin bayani:Siyasar Jamus: Manhajar Tiktok na taka rawar gani ga matasa
Magajin Garin birnin Zapopan Juan Jose Frangie ya nuna takaicinsa kan kisan da aka yi wa matashiyar, kuma ya ce bata sanar da cewa tana fuskantar barazana daga 'yan ta'adda ba.