An bude taron kasashen G7 a Kanada
June 16, 2025A wannan Litinin ake bude taron kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki na G7 a kasar Kanada.
Shugaban Amurka Donald Trump da kuma shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz na daga cikin wadanda suke halartar taron da Firaministan Kanada Mark Carney ke karbar bakonci.
Taron na kwana biyu da ke gudana a birnin Kananaskis zai mayar da hankali ne kan neman cimma matsaya tsakanin kasashen da ke da banbancin ra'ayi kan harkokin kasuwanci da haraji da Amurka.
Wannan dai shi ne karon farko da Trump ke halartar taron tun bayan shiga ofis a wa'adi na biyu na mulkinsa, a watannin da suka gabata shugaban na Amurka ya tada kura bayan kwantsama haraji kan kasashen duniya.
Kungiyar G7 ta lashi takobin karya lagon Rasha kan yakin Ukraine
Masana suna kuma ganin kasashen ka iya tattauna yakin da Isra'ila ke yi da Iran a yayin da lamarin ya fara shafar farashin mai a duniya da kuma jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin rudani.