An buda taron Majalisar Dinkin Duniya
September 25, 2012Shuwagabain kasashen duniya na hallartar taron shekara shekara na majalisar dinkin dunkin duniya a birnin New York na Amurka inda batun da ya fi daukar hankalin shi ne na halin da ake ciki a kasar Siriya da kuma batun makamashin kasar Iran. A lokacin da ya ke jawabinsa ga mahalarta taron shugan kasar Iran Ahmadine Nijad ya nanata cewar kasarsa zata yi amfani da duk wani karfin sojin da Allah ya fuwace mata domin ta kare kanta indan har kasashen Isra'ila da Amurka suka bukaci aukawa kasar,bayan da ya sake maimaita cewar tashoshin nikleyar kasar ya dogara ne ga amfanin samara da makamshinn farar fulla abundas kasahen duniya suka ki amuncewa da shi. Shugaban ya kuma tabo batun luwadi da ya danganta da aloba a duniya da kasashe masu huja jari ke karfafawa inda ya ce babu addini ko al'ada a duniya da ta amunce da saduwar masu jinsi daya,hasali ma ya ce illahiran annabawan Allah sun kalubalanci wannan tabi'ar da kasasahen yammaci suka karfafa.
Mawallafi : Issoufou Mamane
Edita : Umaru Aliyu