An buɗe taron shugabannin ƙasashen Afirka
July 15, 2012An buɗe taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Afirka a birnin Addis Ababa na Ethiopiya bayan taron share fage na ministocin harkokin waje da aka kammala a jiya. Taron wanda ke duba muhimman batutuwa da ke cimma nahiyar tuwo a ƙwarya , waɗanda suka haɗa da na zaɓen shugaban hukumar zartaswa na ƙungiyar da na rikicin Mali da kuma Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ya sanar da cewar a shirye ƙasahen ƙungiyar suke su aike da wata rundunar kiyaye zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa a gabashin jamhuriyar dimokaraɗiyyar Kwango, inda ake fada tsakanin dakarun gwamnatin da na kungiyar m23.
An shirya daura da taron shugabannin ƙungiyar ƙasahen yankin Grand Lak, za su tattauna shawarar, ta haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin ƙungiyar ta AU da kuma Majalisar Dinkin Duniya domin tura rundunar kiyaye zaman lafiyar zuwa Jamhuriyar Dimkardiyar Kwango.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas