An bankado dubban mahajjatan bogi a Saudiyya
June 2, 2025Ana dai aika sakonni da harsunan Larabci da na Turanci bisa tarar da ta kai Riyal dubu 20, a kan duk wani mutumin da aka samu da kokarin yin kutse a cikin hajjin na bana. Kuma kama daga hanyar shiga Makka ya zuwa shi kansa masallacin harami da ke cikin garin dai, ana binciken kwakwaf bisa sahihanci na masu niyyar aikin.
To sai dai Kuma ya zuwa safiyar wannan rana ta Litinin din nan dai hukumomin masarautar Saudiyya sun sanar da korar mutane kusan dubu 295, da suka ce suna kokarin shiga aikin na hajji ta hanyoyi na jabu. Saudiyyar dai ta kuma ceta kame mutane 1,239ko bayan rufe wasu ofisoshin bogi 415 da ke bada izinin yin aikin na hajji na bogi a shekarar bana.
Kokari na neman kutse a cikin aikin dai na ta karuwa tun bayan bullar katin Nusuk da kasar ta ce yana zaman hanya daya tilo ta kaiwa ya zuwa tantance alhazai na gaskiya.
Akasin abun da ke akwai can baya dai, akwai ragi na cikowa a shi kansa masallacin na Makka, inda dubban alhazai a halin yanzu ke ziyarta domin yin Umrah. Akalla mutane 2,717 ne dai suke shirin asarar ta hajji daga tarayyar Najeriyar kadai sakamakon rufe izinin shiga cikin aikin na bana.
Abun kuma da a cewar Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal da ke zaman kwamishinan tsare tsare na hukumar ta alhazan Najeriyar basu da laifi a kansa. Sama da jami'an tsaro 40,000 ne dai ke taka rawa a kokari na tsaftace hajjin a shekarar bana.