Amurka za ta kara wa Ukraine karfin yaki da Rasha
July 14, 2025Talla
Shugaba Donald Trump ya bayyana hakan ne ga 'yan jarida a sansanin soja na Joint Base Andrews da ke a wajen birnin Washington, sai dai bai fayyace adadin makaman da za a tura wa Ukraine din ba.
Ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya "bai wa mutane da dama mamaki" saboda rashin amincewa da batun tsagaita wuta a Ukraine.
Trump ya nuna rashin jin dadinsa game da halin da ake ciki da kuma yadda Putin ke jan kafa wajen samar da zaman lafiya a Ukraine.
A yau Litinin ne dai Shugaba Trump zai gana da Sakatare Janar na kungiyar kawancen tsaron kasashen yammacin duniya NATO, wato Mark Rutte, domin tattaunawa kan batutuwan Ukraine da ma sauran al'amura.