Amurka za ta fara cajar masu yawon bude ido Dala 15,000
August 5, 2025Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar a jiya Litinin da wani shiri na fara cajar masu zuwa yawon bude ido kasar daga wasu kasashe kudin da ya kai Dala 15,000 domin samun biza.
Za a wallafa wannan mataki a kundin dokokin Amurka a yau Talata kuma zai fara aiki daga ranar 15 ga wannan wata na Ogusta a karkashin shirin shugaba Donald Trump na yaki da bakin haure.
Karin bayani: Kotun kolin Amurka ta ba wa Trump damar aiwatar da munufarsa ta korar baki
Wannan shiri da za a aiwatar a tsawon watanni 12 a matsayin gwaji zai shafi 'yan kasashen da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewa suna wuce gona da iri wajen makalewa a kasar bayan cikar wa'adin takardunsu na biza.
Bisa ga wata kididdiga da ma'aikatar harkokin wajen ta Amurka ta fidda, akalla mutane 500,000 ne suka makale a kasar a 2023 bayan bizarsu ta kare, sai dai ba ta yi karin haske kan jerin kasashen ba.