Amurka za ta binciki hadarin jirgin ruwan Mexico
May 18, 2025Jami'an Amurka za su gudanar da bincike kan karo da gadar Brooklyn ta birnin New York da wani jirgin ruwan kasar Mexico ya yi a ranar Lahadi, lamarin da ya haddasa mutuwar ma'aikatan jirgin biyu.
Magajin birnin New York Eric Adams ya fada a ranar Lahadi cewa mutane 277 ne ke cikin jirgin ruwan yayin faruwar al'amarin kuma tuni biyu suka rasu sakamakon raunuka da suka samu.
Mutum bakwai sun halaka a hadarin jirgin sama a Mexico
Akwai wasu 19 da suka tsira amma da raunuka kuma biyu daga cikinsu na nan rai kwakwai mutu kwakwai.
Hukumar tabbatar da tsaron sufuri ta Amurka ta fada a shafinta na sada zumunta cewa ta bude bincike kan hadarin domin sanin musabbabinsa.
An bude wuta kan wata 'yar TikTok a Mexico
Shugabar kasar Mexico Claudia Sheinbaum ta wallafa a shafinta na X cewa ta kadu matuka da rasuwar ma'aikatan jirgin ruwan biyu tare da yi wa iyalansu ta'aziyya.