Amurka ta soke kashi 83 na ayyukan USAID
March 10, 2025A wata mukala da ya wallafa a shafin X wanda aka fi sani da Twitter a da, Rubio ya ce bayan makonni shida da aka dauka ana sake nazarin hukumar, yanzu ta tabbata a hukumance an soke kashi 83 cikin 100 na shirye shiryen hukumar ta USAID.
Ya ce an soke kwangiloli 5,200 wadanda aka kashe biliyoyin kudade akansu ta hanyoyin da basu amfana komai ba, ya ce a wasu bangarorin ma sun cutar da kasa ne musamman ciyar da muradun kasar Amurka gaba.
Ya kara da cewa sauran kwantaragin da suka rage, za a aiwatar da su ne kai tsaye karkashin kulawar ma'aikatar harkokin waje.
'Yan majalisa na bangaren adawa sun baiyana matakin da cewa haramtacce ne, domin yana bukatar amincewar majalisa tukunna.
A shekarar 1961 ne dai aka kafa hukumar ta USAID domin bayar da taimakon jinkai ga sassan duniya da ke cikin tsananin bukata.