Amurka ta kaurace wa taro kan hakkin dan Adam
August 28, 2025Talla
Dukkanin mambobin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, in ban da Amurka sun fitar da sanarwa, inda suka bayyana yunwa da ake fama da ita a Zirin Gaza a matsayin "matsala ta jinkai”, tare da gargadin cewa amfani da yunwa a matsayin makamin yaki ya saba wa dokokin kasa da kasa na jinkai.
Mambobin kwamitin dai na Majalisar Dinkin Duniya, sun nuna damuwa ne tare da alhini mai zurfi bayan rahoton da Hukumar Kimanta Tsaron Abincin Duniya (IPC) ta fitar a ranar Juma'a makon jiya, wanda ya tabbatar da tsananin matsalar abinci a yankin na Gaza.
Isra'ila dai ta bukaci da a goge rahoton da IPC ta fitar nan take, tana mai bayyana shi a matsayin "na kirkirarre” kuma an yi shi ne bisa tasirin siyasa.