Amurka ta kalubalanci Macron kan ayyana kasar Falasdinu
July 25, 2025A daidai lokacin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi shelar cewa zai ayyana Falasdinu a matsayin kasa mai cikakken iko a watan Satumbar 2025.
Karin bayani:Macron: Muna adawa da sake fasalin Gaza
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce wannan mataki ka iya maida hannun agogo baya a yunkurin yarjejeniyar sulhu da kuma kawo karshen yakin Gaza baki daya. Kazalika Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce matakin da Macron ke kokarin dauka babu abin da zai haifar illa nuna goyon baya ga ayyukan ta'addanci.
Karin bayani: Netanyahu ya zargi kawayensa da taimakon Hamas
Shugaba Macron dai ya sanar da cewa zai bayyana Falasdinu a matsayin kasa mai cikakken 'yancin cin gashin kai a lokacin da zai gabatar da jawabi a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a watan Satumbar 2025.
.