Amurka ta janye kayan lataronin Chaina daga sabon haraji
April 12, 2025Ana sa ran matakin ya rage kaifin radadin tashin farashin kayayyakin da zai faru a Amurka bayan da a kwanaki Shugaba Donald Trump ya lafta wa kasashe ciki har da China haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su kasar.
Kayayyakin lataroni 20 ne wannan saukin haraji ya shafa. Sai dai gwamnatin ta Amurka wacce ta sanar da sassaucin ta hannun hukumar kwastam ba ta bayyana dalilin cire harajin ba, inda ake sa ran kamfanonin fasaha na Amurka kamar Apple da Dell za su ci gajiyar hakan matuka, ganin yawancin kayayyakinsu ana hada su ne a China.
Masana sun ce wannan saukin zai rage hauhawar farashi da kuma matsin da masana'antar harkokin fasahar zamani ke fuskanta. Tuni China ta mayar da martani da karin haraji har kashi 125% kan kayayyakin Amurka da ke shiga kasar.