Amurka ta ce za ta daidaita da Turai a kan sabon harajinta
April 18, 2025Talla
Yayin ganawarsu a Washington, Shugaba Donald Trump ya shaida wa firaministar Italiya Giorgio Meloni cewa za a cimma yarjejeniya 100 bisa 100 a tsakanin Amurka da Turai a wani mataki kan harajin, amma kuma ya jaddada cewa babu batun gaggawa a ciki.
Shugaban na Amurka ya ce yana farin ciki da kudaden da gwamnatin kasar za ta rika samu daga kudaden harajin daga kasashen waje.
Daga nata bangare firaministar ta Italiya Giorgia Meloni ta nuna kwarin gwiwar cewa za a cimma daidaito a tsakanin Amurkar da kasashen Turai a game da wannan batu na haraji.
Tun da farko dai Meloni ta soki harajin kashi 20% da Trump ya sanar kan kayayyakin kasashen Turai da za su shiga Amurka, wanda daga bisani ya dakatar na kwanaki 90.