Amurka ta ce ta kashe manyan Jami'an Huthi
March 16, 2025Hare haren da aka kai Sanaa babban birnin kasar da Saada da Al Bayda da Radaa sun hallaka akalla mutane 31 da kuma jikkata wasu mutanen fiye da 100 yawancinsu mata da kananan yara a cewar mai magana da yawun ma'aikatar lafiya na Houthi Anis al-Asbahi.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi ya bayar da umarnin kai harin a daren Asabar ya kuma yi barazanar kai karin wasu hare haren idan yan tawayen basu daina kai hari tekun Bahar Maliya da kuma tekun fasha ba.
Tun dai bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, yan tawayen basu kai wani hari kan hanyoyin ruwan ba, sai dai a ranar Talata sun ce za su ci gaba da kai kan jiragen ruwan Israila.
Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan tsaron kasa Michael Waltz ya shaida wa kafar yada labaran ABC ta Amurka cewa hare haren sun hallaka shugabannin Huthi.
'Yan Huthin wadanda suka kwashe shekaru suna yaki a kasarsu sun lashi takobin mayar da martani.