Amurka ta cafke wasu shugabannin 'yan awaren Kamaru
September 6, 2025Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta ce an gurfanar da mutanen guda biyu Benedict Nwana Kuah da Pascal Kikishy Wongbi, wadanda aka cafke su a jihar Minnesota. Hukumomin Amurka na zargin mutanen biyu da kisan kai da tada zaune tsaye da kuma garkuwa da mutane sauran laifukan sun hada da halasta kudin haram da zamba cikin aminci.
Karin bayani:Najeriya: Harin 'yan Ambazoniya na Kamaru
Babban mai gabatar da kara na Amurka ya ce mutanen biyu Kuah da Wongbi na rike da shugabanci a kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Ambazoniya daga Kamaru.
Karin bayani:'Yan aware sun halaka mutane 20 a Kamaru
Wata kungiya da ke tattara alkaluman wadanda ibtila'i ya afkawa ta sanar da cewa mutane sama da dubu 6,000 ne suka mutu a rikicin yankin Ambazoniya, yayinda wasu sama da miliyan daya suka rasa muhallansu.