SiyasaGabas ta Tsakiya
Amurka na nazari kan sake tsugunar da Falasdinawa a Afirka
March 14, 2025Talla
Amurka da Isra'ila na duba yiwuwar sake tsugunar da al'ummar Gaza sama da miliyan biyu a wasu kasashen gabashin Afirka, a shirin Donald Trump na sauya fasalin Zirin Gaza.
Karin bayani:Taron Larabawa kan makomar Gaza a Masar
Jami'an gwamnatin Sudan sun yi fatali da wannan mataki, yayin da Somaliya da yankin Somaliland da ya balle daga kasar ta Somaliya suka sanar da kamfanin dillancin labaran AP cewa ba su da masaniya kan matakin mayar da al'ummar Gaza kasashensu.
Karin bayani: Kasashen OIC sun goyi bayan Masar kan gina Gaza
Tuni dai Falasdinawa da kasashen Larabawa suka yi fatali da bukatar Trump na rarraba al'ummar zirin a wasu kasashen Gabas ta Tsakiya, kafin daga bisani ya bijiro da zancen mayar da su nahiyar Afirka.