Amurka na bukatar a tsagaita bude wuta a Gaza
June 30, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kiran da a samu ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta a yakin Isra'ila da Hamas a Zirin Gaza, duk da cewa wasu Falasdinawa sun nuna shakku game da yiwuwar cimma sulhu.
Kafin yanzun an ba da labaran cewa Ron Dermer, babban mai bai wa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu shawara, zai kai ziyara Washington a wannan makon domin tattaunawa kan tsagaita wutar, yayin da ake shirye-shiryen Netanyahu zai kuma ziyarci Amurkar cikin makonni masu zuwa, abin da ke nuna alamu na yiwuwar samun ci gaba a yarjejeniyar.
Netanyahu ya gana da majalisar tsaron kasarsa a daren Lahadi don tattauna wasu shirye-shirye da ba a kammala ba, yayin da Shugaba Trump ya yi kira a kafafen sada zumunta da a yi yarjejeniya a Gaza, a kuma sako fursunonin yaki.
Sai dai, har yanzu ana ci gaba da samun hare-haren Isra'ila a Gaza, inda wani harin jirgin yaki ya kashe akalla mutane 15, ciki har da mata da kananan yara, a yankin Jabaliya al-Nazla, wanda ke karƙashin sabon umarnin kaura daga arewacin Gaza.