Amurka na barazanar ya da kwallo a sansancin rikicin Ukraine
April 18, 2025Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi barazanar janye kasarsa daga tattaunawar da ake yi don kawo karshen yakin Ukraine, sakamakon tafiyar hawauniya da matakin ke yi a tsakanin fadojin mulkin kyiv da Moscow. Bayan halartar taron da kasashen Yamma suka gudanar a birnin Paris ne Rubio, ya ce ya zama wajibi a cikin kwanaki masu zuwa ko zaman lafiya ya samu a Ukraine ko a'a. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da alkawarin wata guda da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi na dakatar da hare-haren a cibiyoyin makamashi Ukraine na tsawon kwanaki 30 ya cika.
Karin bayani: Amurka da Rasha na tattaunawa kan yakin Ukraine
A halin da ake ciki ma, wasu sabbin hare-hare da Rasha ta kai cikin dare sun yi sanadin mutuwar akalla mutane biyu tare da jikkata wasu da dama a garuruwan Kharkiv da Sumy na Ukraine. Sai dai, rashin samun ci gaba mai ma'ana a kokarin warware rikicin, ya sa Amurka da kasashen Turai da Ukraine sun yanke shawarar sake haduwa a mako mai zuwa a London don tsayar da matsaya guda.