Cinikin makamai ya karu a duniya a shekara ta 2024
April 28, 2025Kasashe dabam-dabam sun kashe kimanin dala tiriliyan 2.7 kan sojojinsu, karin kusan kashi 9.4 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2023. Wannan shi ne adadi mafi girma na karin kudade da kasashen duniya suka kashe a shekara daya wajen sayo makamai tun bayan kawo karshen yakin cacar baka.
Fiye da kasashe 100 ne dai suka kara kasafin kudinsu na tsaro a shekarar 2024, kamar yadda rahoton cibiyar bincike kan zaman lafiya ta SIPRI ya bayyana.
Babban karin an fi ganinsa a Turai da Gabas ta Tsakiya sakamakon ci gaba da yakin Ukraine da kuma rikicin Gaza.
Alal misali tun bayan hadewar Jamus, a shekarar da ta gabata ne kawai kasar ta karbi lakabin zama kasar da za ta zarta sauran kasashen yamamcin Turai kashe kudade wajen sayen makamai, a cewar cibiyar ta SIPRI
A shekarar 2024, kasafin kudin sojin Jamus ya karu da kashi 28 cikin dari zuwa dala biliyan 88.5, hakan ya sa Jamus ta hau matsayi na hudu a duniya, bayan Amurka, China, da Rasha.
A fadin Turai, ana ci gaba da kara kasafin kudin tsaro. Poland ta kara da kashi 31 cikin dari, yayin da Sweden da yanzu ta shiga kungiyar tsaro ta NATO ta karu da kashi 34 cikin dari.
Jean-Brice Dumont daga kamfanin Air Power Airbus, daya daga cikin manyan masu kera makamai a Turai, ya bayyana yadda suke sarrafa makamai don cika bukatun Turai.
"Mun fara daga inda Turai ke siyan mafi yawan kayan tsaronta daga kasashen waje. Wannan wani abu ne da dole mu sauya. Mun dauki dogon lokaci muna neman ‘yantar da kanmu a harkar sarrafa makamai, amma dole a fara yanzu. Yanzu muna ganin yadda Turai ke saka kudi don samar da kayanta na tsaro na yau da gobe."
Ukraine ita ce ta fi kasa jin jiki a wannan harka, inda ta kashe kashi 34 cikin dari na tattalin arzikinta na GDP dinta kan tsaro. A daya bangaren kuma, kasafin kudin sojin Rasha ya karu da kashi 38 cikin dari zuwa kusan dala biliyan 150.
A Gabas ta Tsakiya kuwa, Isra'ila ta fi kowacce kasa karin kashe kudin soji, inda ta samu karin kashi 65 cikin dari, saboda rikicin da Hezbollah da kuma yakin Gaza.
Xiao Liang, wani masani daga cibiyar SIPRI,ya ce bai yi mamakin wannan karuwa daga Isra'ila ba.
"Mun ga yadda kashe kudin Isra'ila ya karu sosai tun farkon yakin Gaza a Oktoba 2023 da kuma sabon yakin Kudancin Lebanon a Oktoba 2024. Makomar kasafin kudin Isra'ila za ta dogara ne kan sakamakon yarjejeniyar tsagaita wuta a Gabas ta Tsakiya. A kan Iran da wasu kasashe kuwa, abin da aka za ta na karin kashe kudi bai faru a 2024 ba."
To shin me ya faru da Amurka a 2024? Har yanzu ita ce ke da mafi girman kashe kudin soja a duniya, inda ta ware kusan dala tiriliyan guda, tana mai da hankali sosai wajen sabunta makaman nukiliyarta da kimtsa kanta bisa Rasha da China.
A Asiya kuwa, China ta ci gaba da sabunta sojojinta, inda ta kashe dala biliyan 314 yayin da Japan ta kara kasafinta da kashi 21 cikin dari.