SiyasaUkraine
Amurka da Ukraine sun cimma yarjejeniya
May 1, 2025Talla
Amurka da Ukraine sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar ta samar da kudade don sake gina kasar da yaki ya daidaita. Gwamnatocin biyu sun tabbatar da hakan a Washington.
Kawo yanzu dai Amurka ba ta fidda cikkaken bayanin yarkejejeniyar ba, sai dai an yi amannar cewa yarjejeniyar za ta bai wa Amurka damar cin moriyar albarkatun kasa na Ukraine wanda ke da matukar muhimmanci ga kamfanonin fasaha na Amurka.
A waje guda mataimakiyar Firaministan Ukraine kuma Ministar tattalin arziki Yulia Svrydenko ta ce Ukraine za ta ci gaba da yin iko da albarkatunta a cikin yarjejeniyar da Amurka.
Sai dai kuma shugaba Trump da yake jawabi ga yan jarida, ya ce Amurka za ta amifana da Ukraine fiye da gudunmawar da ta bayar.