Amurka da Saudiyya sun bukaci a kawo karshen yakin Sudan
April 10, 2025Amurka da Saudi Arebiya sun bukaci a koma teburin tattaunawar kawo karshen yakin basarar Sudan da yanzu haka ke cika shekaru biyu ana gwabzawa, tsakanin sojojin kasar da dakarun RSF na Mohamed Hamdan Dagalo. Kasashen biyu sun yi wannan kira ne bayan ganawar da ta wakana a Washington, tsakanin sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da takwaransa na Saudi Arebiya Yarima Faisal bin Farhan, inda suka ce tattauwar sulhun ta zama tilas, don kare fararen hula tare da bude kofar shigar da agaji kasar, sannan a mayar da ita kan turbar Dimukuradiyya.
karin bayani:Sojojin Sudan sun kashe mutane da dama a harin kasuwar Tora
Sudan dai ta jaddada zargin da take yi wa Hadaddiyar Daular Larabawa na hannu dumu-dumu a cikin yakin basarar kasar na tsawon shekaru biyu, ta bakin ministan yada labaranta Khalid al-Aiser. A Alhamis din nan ce kotun duniya ICJ za ta saurari korafin da Sudan ta shigar tana zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da haddasa kisan kiyashi, ta hanyar tallafa wa dakarun RSF da makamai, ko da yake ta jima tana musanta aikata hakan.
karin bayani:AU ta yi gargadi kan hadarin da ke tattare da gwamnatin RSF
Rikicin dai ya yi sanadiyyar mutuwar dubban jama'a tare da tilasta sama da miliyan goma sha biyu tsere wa daga gidajensu, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shi a matsayin yanayin jin kai mafi muni a duniya.