Amurka da Japan sun cimma yarjejeniyar kasuwanci
July 23, 2025Talla
A sabuwar yarjejeniyar da Trump ya kira mafi girma a tarihin kasashen biyu, ya ce a karkashinta Japan za ta saka hannun jari a kasarsa na sama da biliyan 550 na dalar Amurka kuma Amurkawa da dama za su samu ayyukan yi.
Trump ya yi barazanar sanya haraji kan kasashe da dama, idan ba su sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci da Amurka nan da wata mai zuwa ba.
Ya zuwa yanzu, Trump ya rattaba hannu kan yarjejeniyar harajin kasuwanci da Japan da Burtaniya da Vietnam da Philippines da Indonesia, tare da tattaunawa da sauran abokan hulda.
Karin Bayani: Wakilin EU zai je Washington don tattauna harajin Trump