Amurka da EU sun cimma yarjejeniyar kasuwanci
July 28, 2025Yarjejeniyar kasuwanci da aka cimma tsakanin Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai ta kawo karshen takun-saka da aka kwashe tsawon watanni ana yi a kan kudin haraji. Wannan ci gaban na zuwa ne bayan da Shugaba Donald Trump na Amurka da kuma Shugabar hukumar zartarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leye suka yi wata ganawa a Scotland. Shugaba Trump ya yi maraba da yarjejeniyar inda ya ce ta yi wa dukanin bangarorin biyu dadi. A nata bangaren Von der Leyen, ta ce yarjejeniyar ta kawo kwanciyar hankali a yanzu.
Karin bayani: EU za ta yi wa shugaba Trump na Amurka martanin karin haraji
An amince da biyan harajin kashi 15 cikin dari kan kayayyakin Turai, rabi adadin da Shugaba Trump ya yi ikrarin laftawa a baya. Tarayyar Turai ta kuma ce za ta zuba jari a fannin makamashin da kuma makaman yakin Amurka.