CinikiChaina
Amurka da China za su dakatar da karin haraji
May 12, 2025Talla
Matakin na zuwa ne bayan da shugaba Donald Trump ya nuna alamu a karshen mako cewa tattaunawar cinikayya da Beijin na gudana lami lafiya.
Ya ce sun cimma yarjejeniyar jinkirtawa juna na kwanaki 90. Sakataren baitulmalin Amurka Scott Bassent ya shaida wa yan Jarida cewa bangarorin biyu za rage kudin fiton su kasa da kashi 115.
Ya kara da cewa Amurka na da sha'awar samun daidaito a cinikayya da sauran kasashe kuma za ta ci gaba da yin hakan.
A nata bangaren Beijin ita ma ta sanar da samun ci gaba a tattaunawar a Washington.