Amurka da China sun tattauna rikicin kasuwancinsu
May 11, 2025Tattaunawar ta kwanaki biyu da aka kamala, mai baiwa fadar mulkin Amurka shawara a kan tattalin arziki Kevin Hassett ya bayyana alamun haske a hadin kan da China ke kokarin bayarwa.
Shi ma a nashi bangaren a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta Shugaba Donald Trump na Amurka ya tabbatar da kyakyawar fahimtar juna a tattaunawar da aka yi a tsakanin jami'an kasashen biyu. Trumpya ce mafi akasarin abubuwan da aka tattauna a wannan taro na Geneva an amince da su.
Wannan dai ita ce tattaunawa ta farko tsakanin Beijing da Washington tun bayan da sabon harajin na Trump ya soma aiki a watan da ya gabata.
Rikicin kasuwanci da ya barke a tsakanin kasashen mafiya karfin tattalin arziki a duniya ya janyo koma baya ga tattalin arziki a fanni daban-daban na duniya.
Karin Bayani:Yakin kasuwanci tsakanin China da Amurka ya fara gadan-gadan