Amirka za ta yi gwajin makami mai linzami
August 3, 2019Talla
Tun a watan Fabrairu Amirka ta fara barazanar fita daga yarjejeniyar kan zargin Rasha da rashin biyayya, abin da kasar Rasha ta karyata.
A shekarar 1987 tsohon Shugaban Amirka Raonald Reagan da tsohon shugaban tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev suka amince kan yarjejeniyar lalata makaman nukiliyar karkashin kasa masu cin zango tsakanin kilomita 500 zuwa 5,500.