Tattaunawar takaita manyan makamai
July 28, 2021Talla
Wannan zama tsakanin Moscow da Washington na kasancewa ci gaba a kan wanda shugabannin kasashen biyu suka fara a watan Yuli. Za a tattauna batun kayyade mallakar makamai sai dai zaman na zama na sirri da ba zai sami halarta 'yan jarida ba.
Za a kwashe wunin guda ana wannan zaman tsakanin mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amirka Wendy Sherman da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov.
Rikicin diflomasiya tsakanin kasashen biyu ya jima da yna jawo tarnaki wanda ko a baya-bayan nan Amirka ta gargadi Rasha a kan kutsen da ake zargin ta yi a wasu kafafen na intanet.