Jamus ta janye daga batun bututun Rahsa
September 8, 2020Talla
Da yake jawabi ga manema labaru a fadar White House a jiya Litinin game da shirinsa na rufe tashoshin makamashin kwal da na nuclear, shugaban Amirkan ya ce, Jamus na matsayi mai rauni idan aka zo batun makamashi, kuma yanzu sun saka kansu a cikin wani hali na tsaka mai wuya.
A nasu bangaren, kakakin shugabar gwammnati Angela Merkel, ya ce akwai yiwuwar Jamus ta dauki wannan matakin, a matsayin martaninta kan amfani da guba a kan jagoran adawar Rashar Alexei Navalny.
An dai kusan kammala aikin bututun dakon makamashin.