Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane fiye da 100 a kudancin Rasha
July 7, 2012Talla
Mutane fiye da dari daya ne suka rasu bayan aukuwar ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma ambaliya a yankin shakatawa na kogin Black Sea a kudancin Rasha. Ruwan saman wanda aka kwashe kwanaki biyu ana tafkawa ya haifar da ambaliyar wadda ta mamaye gidaje kimanin 5,000 yayin da mutane fiye 22,000 ke zaune a cikin duhu saboda katsewar wutar lantarki. Wani Gwamnan lardi a yankin Alexander Tkachev ya baiyana ambaliyar da cewa ita ce mafi muni a tsawon lokaci da dama. A yanzu dai an sanya dokar ta baci a birane da dama a yankin. Firamininstan Rasha Dmitri Medvedev ya umarci Ministan ayyukan gaggawa Vladmir Puchkov ya jagoranci ayyukan ceto da taimakon jin kai.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Zainab Mohammed Abubakar
.