SiyasaArewacin Amurka
Ambaliyar ruwa ta halaka mutane da dama a Texas na Amurka
July 5, 2025Talla
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa wajen kai dauki yankin na Texas, inda ya ce shi da mai dakinsa Melenia na mika sakon jaje da ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu. Trump ya kara da cewa jami'an hukumar kashe gobara da sauran jami'an agaji na ta fadi tashin kubutar da al'umma tare kuma da kokarin dakile tasirin ambaliyar.
Karin bayani:Ambaliyar ruwa ta tsananta a wasu jihohin Amurka
Baturen 'yan sandan yankin Kerr County, ya sanar da cewa masu aikin ceto sun yi nasarar kubutar da mutane sama da 800.