SiyasaChaina
Ambaliya ta kashe mutane 30 a China
July 29, 2025Talla
Mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi ajalin mutane 30 a arewacin China tare da tilasta kwashe mutane fiye da 80,000 zuwa Beijing babban birnin kasar.
Jaridar Beijing Daily ta ruwaito cewa ruwan saman ya haddasa rufe hanyoyi da dama da kuma katsewar lantarki a kauyuka sama da 130 yayin da jami'an agaji ke ci gaba da aikin ceto.
A ranar Litinin da daddare, shugaban kasar Xi Jimping ya bukaci mahukuntan yankunan da ke fuskantar hadarin ambaliyar da su gaggauta samar da tsare-tsare domin kubutar da jama'a.
A yanzu haka ana hasashen samun saukar mamakon ruwan sama har zuwa gobe Laraba a wasu yankuna sama da 10 na China.