Bukukuwan sabuwar shekara 2025
January 1, 2025Al'ummomin duniya na sassa dabam-dabam sun gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara ta 2025 cikin anashuwa da nishadi. Daga Sydney zuwa Paris, Damascus ko Tibilisi, daga New york, zuwa Bangkok, duniya na murnar shiga sabuwar shekarar. Daga daran Talata zuwa Larba a birane da dama an gudanar da wasan wuta da sauran shagulgula a karshen shekarar da ta kasance cike da abin al ajabi. Na iftalai sakamakon dumamar yanayi, tun daga tsananin zafin da aka yi na aikin hajji, zuwa bala'in ambaliyar ruwa. Da yake-yake a yankin Gabas ta tsakiya, da kuma sake dawowar Donald Trump kan karagar mulki wanda ake cikin fargaba: Da yake yin jawabi na barka da sabuwar shekara shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya yi kiran da a ba da hadin kai, ko da ma ana cikin mayan kalubale: ''Ya ku 'yan kasata, wannan shi ne mu. Jamus ke nan. Mu, ba kasa ce ba ta gaba, kasa ce ta hadin kai, ta haka za mu iya samun ƙarfi, musamman a lokuta masu wahala irin waɗannan. Kuma lokuta suna da wahala. Duk muna jin haka. Tattalin arzikinmu yana ja da baya.