A Jamus Igbo sun yi bikin kakar sabuwar doya
August 14, 2025Bikin kakar sabuwar doya na daya daga cikin biki mafi girma na Kabilar Igbo wadanda suka fito daga yankin kudu maso gabashin Najeriya duk da cewa akwai tsatson kabilar a kasashe irin su Kamaru da Benin da Burkina Faso da Togo da dai sauransu. Tarihi ya nuna cewa abin kunya ne a al'adar Igbo, manomi ya girbe doyarsa ko ya ci, ko ya sayar a kasuwa kafin gudanar da wannan biki na sabuwar kakar doya da aka fi sani da ‘New Yam Festival'.
Birnin Cologne ya yi cikar kwari da baki daga ciki da wajen Tarayyar Jamus musamman daga Amurka da Belljiyam da Faransa da kuma sauran kasashen nahiyar Turai da Amurka. Guda daga cikin Sarakunan Kabilar Igbo mazaunin Jamus Cif Charles Geanikai-Nhyoma, ya yi karin haske dangane da muhimmancin bikin ga Kabilar Igbo a duk inda suke a fadin duniya.
‘' Muna kokarin dabbaka al'adunmu da muka gada tun kaka da kakanni, domin mu ci gaba da tafiyar da al'adar daga karni zuwa karni. Kuma hakan na nuna jajircewarmu da zaman lafiya da hadin kai. Kuma muna gudanar da wannan biki ne a duk shekara domin godiya ga mahaliccinmu kuma a bana muna godiya ga Allah kasancewar a bana muna gudanar da wannan biki a yammacin duniya.
A yayin bikin na kakar sabuwar doya ana gudanar da wasu tsarabe-tsarabe da tsatsube-tsatsube na al'adar gargajiyancin Kabilar Iggbo da ya kunshi rawa da waka da kuma kaddamar da gidauniyar ci gaban al'ummar Iggbo a fadin duniya.
Shugaban kungiyar kabilar na birnin Cologne Ohaneze Ndigbo Cif Nze Prince Kelvin Obichire ya ce ‘yan Kabilar Igbo jajirtattun mutane ne kuma ba cima zaune ba ne, ta la'akari da shigarsu ta al'ada da ke nuna cewa su jarumai ne.
‘' Aamar tambarin zaki ga al'ummar igbo na nufin Kabilar Igbo jajirtattu ne, muna gudanar da al'amuranmu kamar zaki, bama ja da baya dangane da kalubale kuma muna kaunar kabilun da ke tare da mu Yarbawa da Hausawa kuma dukkanninmu mun zama daya.
Tsohon jami'in diflomsiyyar Jamus da ya yi aiki a karamin ofishin jakadancin Jamus da ke Legas a Najeriya ya ce al'adun kabilar Igbo da kuma abincinsu na daga cikin abin da yake matukar alfahari da shi a tarihin rayuwarsa ta diflomasiyya.
‘'Sunana Michiel Dirus ni tsohon jami'in diflomasiyyar Jamus ne na tsawon shekaru 35, na yi aiki sosai a kasashen kudu da hamadar Sahara. Kuma ina mai tabbatar maku da cewa ‘yan Najeriya mutane ne masu karamci da girmama baki, suna haba-haba da baki da abokanan arziki. Da zarar ka yi mu'amala da dan Najeriya nan da nan zai zama abokinka''
'Yan siyasa da shugabannin al'umma na daga cikin rukunin mutanen da suka halarci taron daga cikin har da dan majalisar dokokin Cologne da ‘dan takarar magajin garin birnin Cologne a jam'iyyr CDU John Emeka Akude wanda shi ma ya fito ne daga tsatson Kabilar Igbo a Najeriya.